![]() |
|
2019-09-07 16:24:10 cri |
Robert Mugabe mai shekaru 95, ya mutu ne da safiyar jiya Juma'a a kasar Singapore, inda ake duba lafiyarsa tun cikin watan Afrilun da ya gabata.
Da yake gabatar da jawabi ga al'ummar kasar, Emmerson Mnangagwa ya ayyana ranekun zaman makokin a kasar har zuwa lokacin binne marigayin.
Ya ce jam'iyyarsu ta ZANU PF, ta yanke shawarar karrama marigayin da lambar yabo mafi daraja ta kasar, wanda ya ce, ya cancanci a ba shi.
Ya kuma yabawa gwamnatin Singapore dangane da irin kulawar da aka ba shi har zuwa lokacin mutuwarsa.
Emmerson Mnangagwa, ya kuma jinjinawa Mugabe bisa irin gudunmawa da sadaukarwar da ya yi domin ci gaban kasar kafin, da bayan samun 'yancin kanta. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China