Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugabannin kasashen Afirka 11 sun tabbatar da halartar jana'izar Mugabe
2019-09-12 20:40:26        cri
Shugaba Emmerson Mnangagwa na kasar Zimbabwe, ya bayyana a yau Alhamis cewa, yanzu haka shugabannin kasashen Afirka 11 ne suka tabbatar za su halarci faretin jana'izar tsohon shugaban kasar marigajyi Robert Mugabe da aka shirya gudanarwa ranar Asabar a babban filin wasa na kasar.

Mnangagwa, bisa rakiyar wasu mambobin jam'iyyar ZANU-PF mai mulkin kasar da shugabannin rundunonin sojan kasar, sun ziyarci iyalan marigayi Mugabe a yau Alhamis, domin yi musu ta'aziyyar Mugabe wanda ya rasu ranar Jumma'ar da ta gabata.

Sai dai shugaban kasar ya karyata rahotanni da kafafen sada zumunta ke watsawa cewa, ya tattauna da sarakunan gargajiya da suka ziyarce shi a farkon wannan mako, ta yadda za su shawo kan gwamnati kan wurin da ya dace a binne Mugaben.

Ita dai gwamnati na son a binne shi a makabartan da ake binne mazan jiya dake Harare, a hannu guda kuma wasu daga iyalansa, na son ganin an martaba wasiyar da ya bari, cewa a binne shi a kusa da mahaifiyarsa a kauyensu dake Zvimba.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China