Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan Zimbabwe sun yi ban kwana da marigayi Mugabe
2019-09-13 16:26:11        cri

A jiya Alhamis ne uwar gidan tsohon shugaban kasar Zimbabwe marigayi Robert Mugabe, wato Grace Mugabe, ta jagoranci dubban al'ummar kasar wajen kallo da ban kwana da gawar marigayin, a filin wasa na Rufaro dake birnin Harare, fadar mulkin kasar.

Taron ban kwana da tsohon shugaban dai na daga cikin tarukan makoki da aka shirya a kasar, wadanda za a ci gaba da gudanarwa har zuwa ranar Asabar.

Masu makokin da suka kunshi manyan jami'an gwamnati, da 'yan jam'iyyar ZANU-PF mai mulkin kasar, da ma sauran talakawan kasar daga yankuna 5 na lardunan kasar 10, sun yi dafifi a filin wasan mai tsohon tarihi, kasancewar sa wurin da tsohon shugaba Mugaben ya yi rantsuwar kama aiki, a matsayin zababben shugaban kasar na farko, bayan samun 'yancin kan kasar ta a watan Afirilun shekarar 1980.

Bisa shirin gwamnatin kasar, za a binne gawar Mugabe a ranar Lahadi, bayan taron jana'iza da zai gudana a filin wasa na Rufaro tsakanin ranekun Alhamis zuwa Juma'a, da kuma wani na daban da za a gudanar a filin wasa na kasa dake birnin na Harare a ranar Asabar.

Ana dai sa ran taron makokin na ranar Asabar, zai samu halartar wasu daga shugabannin kasashe, da manyan baki daga kasashen waje, da jami'an ofisoshin diflomasiyya, da sauran masu makoki 'yan kasar.

A jiya Alhamis, kakakin iyalin marigayin Mr. Walter Chidhakwa, ya shaidawa masu makokin cewa, za a sanar da wurin da za a binne gawar tsohon shugaban na Zimbabwe a cikin karshen mako.

A ranar Juma'ar makon jiya ne dai Mugabe ya riga mu gidan gaskiya, bayan ya yi fama da jinya a kasar Singapore, inda ya rasu yana da shekaru 95 a duniya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China