Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a yi jana'izar tsohon shugaban Zimbabwe ranar Lahadi
2019-09-09 20:24:15        cri
Rahotanni daga kasar Zimbabwe na cewa, a ranar Lahadi mai zuwa ne, za a yi jana'izar tsohon shugaban kasar marigayi Robert Mugabe.

Wata sanarwar da aka rabawa jami'an diflimasiya dake kasar, ta ruwaito ma'aikatar harkokin wajen kasar na cewa, za a gudanar da addu'o'in jana'iza ga Mugabe a babban filin wasan kasar, kafin a binne shi washe gari.

Sai dai ma'aikatar ba ta bayyana wurin da za a binne Mugabe, mutumin da aka ayyana a matsayin gwarzon kasar ba.

A cikin takardar, ma'aikatar ta ce, ya kamata shugabannin kasashe da gwamnatoci dake son halartar bikin addu'o'in na ranar Asabar, su iso Harare a ranar Jumma'a.

Mugabe ya mutu ne ranar 6 ga watan Satumba a kasar Singapore, inda yake jinya tun a watan Afrilu. Ya mutu yana da shekaru 95 a duniya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China