Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi: Amurka na kokarin janyo ruwan dafa kanta
2019-08-22 19:57:59        cri
A jiya Laraba, ma'aikatar tsaron Amurka ta sanar da majalisar dokokin kasar a hukumance cewa, tana shirin sayar wa yankin Taiwan jiragen saman yaki na zamani kirar F-16 guda 66, wadanda kudinsu ya kai dalar Amurka biliyan 8, tare kuma da wasu na'urorin da abin ya shafa. A game da wannan, kasar Sin ta bayyana rashin amincewarta, kuma ta ce za ta dauki dukkan matakan da suka wajaba, ciki har da kakaba wa kamfanonin kasar Amurka dake hannu a wannan cinikayyar.

A hakika, sayar wa Taiwan makamai ba harkar kasuwanci ne kawai ba, amma mataki ne na siyasa da aka dauka a kokarin keta 'yanci da hurumin kasar Sin da kuma tsoma baki a harkokin cikin gidanta,kuma matakin da ko kadan kasar Sin ba za ta hakuri ba, kuma tabbas za ta mayar da martani. Idan har Amurka ba ta canja matsayinta kan wannan batu, to tamkar tana kokarin janyo ruwan dafa kanta ne. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China