Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi gasar "Dream Star" ta karshe na shekarar 2019 a Zimbabwe
2019-09-01 16:21:13        cri

A daren jiya Asabar, kungiyar Sinawa dake Zimbabwe ta gabatar da gasar "Dream Star" ta karshe na shekarar 2019 a cibiyar taro ta kasa da kasa ta Harare, fadar mulkin Zimbabwe. Rukunoni 17 sun yi takara a gasar, inda aka shakata da wakoki da raye-raye masu gamsuwa.

Bayan takarar karo biyu da suka yi, mawakiya Monalisa ta fi samun karbuwa ta samu lambar zinari, hakan ya sa ta zama mace ta farko da ta cimma wannan nasara. Ita da sauran 'yan wasa za su tashi zuwa kasar Sin don nuna fasahohinsu da yayata al'adun Zimbabwe, ta yadda za a kara zurfafa mu'ammalar al'adun tsakanin kasashen biyu.

Jakadan Sin dake Zimbabwe Guo Shaochun, ya taya 'yan wasan da suka samu lambobin yabo murna cewa, yin mu'ammala da hadin kai ta fuskar al'adu wani muhimmin mataki ne na zurfafa hadin kan kasashen biyu a fannoni daban-daban, "Dream Star" wata muhimmiyar alama ce ta hadin kan al'adu, ta samarwa matasan Zimbabwe wani dandali mai kyau na nuna fasahohinsu da cimma muradunsu, ya zuwa yanzu, matasa fiye da 200 sun samu damar nuna fasahohinsu a kasar Sin. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China