Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zimbabwe na fatan Sin da Amurka za su daidaita takaddamar ciniki dake tsakaninsu
2019-06-28 10:36:11        cri

Takaddamar da kasar Amurka ta tayar tsakaninta da kasar Sin, ba ma kawai ta lahanta moriyar kasashen biyu ba, har ma ta kawo babbar illa ga sauran kasashe da yankuna. Yanzu haka, kasar Zimbabwe na kokarin farfado da tattalin arzikinta, don haka kasar take matukar bukatar Sin da Amurka su daidaita wannan matsala cikin lumana, matakin da zai taimaka ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya da ma biyan muradun jama'ar kasar. Rahotanni na cewa, kakakin jam'iyyar African National Union-Patriotic Front dake shugabanci a Zimbabwe, Mista Simon Khaya Moyo ya nuna cewa, Zimbabwe na goyon bayan matakin da Sin take dauka na tinkarar rikicin da Amurka ta tayar, tare da jinjinawa matsayin da Sin take dauka na warware matsalar ta hanyar yin shawarwari.

Ya ce, Sin da Amurka za su amfana da juna a maimakon yin asara saboda hada kansu sosai, kuma tsananta takaddamar dake tsakaninsu za ta kawo mummunar illa ga kasashen Afrika masu tasowa. A cewarsa, an samu gagarumin ci gaba a tattaunawar da Sin da Amurka suka yi, kuma sassan biyu sun cimma matsaya kan batutuwa da dama, amma saboda yadda kasar Amurka ta saba wasu yarjejeniyoyi da suka cimma da ma daukar wasu tsauraran matakai, har ta matsawa kasar Sin lamba mai tsanani. Ya kuma kara da cewa, tattalin arzikin kasar Sin na samun bunkasuwa a cikin shekaru 40 da suka gabata tun bayan da ta yi kwaskwarima a gida da bude kofa ga ketare, duk da wasu kalubalolin da take fuskanta ciki hadda yadda yanayin cinikayyar kasa da kasa ya yi muni kwarai, amma Sin ta tabbatar da bunkasuwar tattalin arzikinta saboda matakan da take dauka, ciki hadda rage haraji da kara bude kofa ga ketare da sauransu. Ya ce, tattalin arzikin Sin yana samun bunkasuwa, don haka yana da kwarin gwiwa kan makomar tattalin arzikin kasar ta Sin. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China