Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zimbabwe ta ce matsin kasashen yamma bai razana ta ba
2019-08-30 12:39:35        cri
Mataimakin shugaban kasar Zimbabwe, Kembo Mohadi, ya ce kasar bata razana da matsin da take fuskanta daga kasashen yammacin duniya ba.

Da yake ganawa da manema labarai bayan ganarwarsa da wakilin MDD a kasar mai barin gado, Bishow Parajuli, mataimakin shugaban kasar ya ce ba abun mamaki ba ne yadda wasu kasashen yamma suka aminta da karairayin da suke fada akan kasarsa.

Kamfanin dillancin labarai na kasar Ziana, ya ruwaito Kembo Mohadi na cewa, akwai wasu mambobin MDD, musammam na kasashen yamma, da suka shafawa kasarsa bakin fenti, kuma suka aminta da abun da suke fada. Amma kuma wadanda suka je Zimbabwe suka shaida abubuwa da idanunsu, su fahimci cewa kasar ta bambanta da abun da ake fada.

Ya ce duk da rashin samun goyon baya daga kasashen yamma, Zimbabwe za ta sake mikewa tsaye.

Har ila yau, ya ce kasar na da juriya, kuma za ta samo mafita da kanta, ko ba tare da kasashen yamma ba, yana mai cewa, daga baya, za su shiga cikin masu yaba mata.

Mataimakin shugaban na mayar da martani ne dangane da sukar da Tarayyar Turai da wasu kasashen yamma suka yi, game da yadda Zimbabwe ta tafiyar da 'yan adawa masu zanga zanga a baya bayan nan.

Ya kuma jinjinawa kyakkyawar dangantakar dake tsakanin Zimbabwe da MDD, wadda ya ce ta taimakawa kasar sosai a lokacin da mahaukaciyar guguwar Idai ta auka mata a watan Maris na bana. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China