Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Alibaba ya kaddamar da shirin samar da horo ga dalibai masu digiri na farko a fannin cinikayya ta yanar gizo
2019-09-12 09:15:30        cri

Katafaren kamfanin nan na hada hadar cinikayya ta yanar gizo na kasar Sin wato Alibaba, ya kaddamar da wani kwas ga dalibai masu karatu a matakin digirin farko, a fannin cinikayya ta yanar gizo domin daliban nahiyar Afirka.

A ranar Talata ne dai dalibai 22 daga kasar Rwanda, suka isa birnin Hangzhou helkwatar kamfanin dake gabashin kasar Sin domin fara wannan kwas, a daidai gabar da kamfanin na Alibaba ke cika shekaru 20 da kafuwa.

Da yake tsokaci game da hakan, shugaban tsangayar koyar da kasuwanci ta Alibaba dake jami'ar Hangzhou Normal University Zeng Ming, ya ce bisa tsari da aka tanada, dalibai daga kasashen Afirka na da damar samun kwarewa a fannonin amfani da yanar gizo, ko cinikayyar kasa da kasa ta yanar gizo. Za kuma su samu zarafin samun horo game da irin ci gaba da Sin ta samu a fannin raya tattalin arziki ta amfani da fasahar sadarwa.

Daya daga daliban da suka samu gurbi a wannan kwas Mike Manzi mai shekaru 18 da haihuwa, ya ce bayan kammala karatun sa, yana fatan kafa wani dandalin cinikayya ta yanar gizo a kasar sa, wanda zai taimaka wajen rage wahalhalun biyan haraji da na kudaden kwastam, da ma na fiton hajoji da ake fuskanta yayin cinikayyar kasa da kasa.

Shirin samar da horon mai lakabin eWTP, bangare ne na yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin gwamnatin kasar Rwanda da kamfanin Alibaba, wanda ya samo asali daga shirin bunkasa hada hadar cinikayya ta amfani da fasahohin sadarwa na kasa da kasa ko eWTP a takaice.

A watan Oktoba na shekarar 2018 da ta gabata ne dai, kamfanonin Wanda da Alibaba na kasar Sin, suka kaddamar da shirin na eWTP a kasar Rwanda, wanda ya baiwa kasar damar zama ta farko daga Afirka da ta kaddamar da wannan shiri. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China