Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta saukakawa matafiya 'yan kasashen waje tsarin samun lasisin tuki na wucin gadi
2019-09-10 20:23:37        cri
Ma'aikatar kula da tsaron jama'a ta kasar Sin, ta bayyana cewa, daga ranar 20 ga watan Satumban wannan shekara, za a saukakawa matafiya 'yan kasashen waje matakan neman lasisin tuki na wucin gadi da suke nema a kasar, inda za a rika ba su na dogon wa'adi.

Liu Yupeng babban jami'i a ma'aikatar ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai, yana mai cewa, duk matafiyin da ya gabatar da takardar neman lasisin tuka mota ko babur na wucin gadi, ba sai ya gabatar da takardar bayanin koshin lafiya ba. Muhimman takardun da ake bukata, sun hada da fasfo, lasisin tuka mota na kasar da mutum ya fito sannan a fassara su cikin harshen Sinanci.

Liu ya ce, daga yanzu wa'adin lasisin zai kasance na abin da bai gaza watanni uku ba, za kuma a iya kara wa'adin zuwa shekara guda, idan har mai lasisin zai zauna a kasar Sin na sama da watanni uku.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China