Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta dauki karin matakan kyautata rayuwar alumma
2019-09-12 08:52:39        cri

Mahukuntan kasar Sin sun sha alwashin daukar karin matakan kyautata rayuwar al'umma, ciki hadda batun samar da ayyukan yi, da inganta farashin abinci, da biyan cikakkun kudaden fanshon tsofaffi.

Wata sanarwa da taron majalissar zartaswar kasar karkashin jagorancin firaminista Li Keqiang ya fitar, ta ce gwamnatin Sin za ta kara baiwa sassa masu zaman kan su tallafi, ta yadda za su zuba jari a fannin raya ilimi, da na kula da lafiya, da fannin ba da hidima ga tsofaffi da kananan yara.

Taron ya kuma amince da sanya magungunan ciwon hawan jini da na sukari, cikin jerin magungunan da kasar ke samarwa inshorar kula da lafiyar al'umma, inda daga yanzu za a rika mayarwa masu fama da cututtukan sama da kaso 50 bisa dari na adadin kudaden maganin da suka saya.

Wannan dai mataki zai rage tsadar biyan kudaden magunguna ga marasa lafiya da yawan su ya haura miliyan 300, karkashin shirin kasar na inshorar lafiya. Kaza lika za a dauki matakai na ingantawa, da rage farashin magungunan cututtukan na sikari da hawan jini da ake sarrafa a cikin kasar ta Sin. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China