Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin Na Kara Jawo Hankulan Jarin Waje
2019-09-10 21:22:13        cri
A yayin taron zuba jari da cinikayya na kasa da kasa na shekarar 2019 da yanzu haka ke gudana a birnin Xiamen na kasar Sin, jimilar jarin waje na kwangilolin da aka sanya hannu a yayin taron tattauna cinikayyar amfanin gona da kayayyakin aikin gona game da shawarar "Ziri daya da hanya daya"da aka gudanar a ranar 8 ga wata ta kai dala biliyan 29.5, kididdigar da ta nuna cewa, kasar Sin na kara jawo hankulan jarin waje.

Babbar kasuwar kasar Sin, shi ne yake jawo wa kasar jarin waje, baya ga haka, cikakken tsarin sana'o'i, yawan jama'a, manyan kayayyakin more rayuwar jama'a da kuma tsarin sufurin kayayyaki mai kyau, kana da aniyyar kasar Sin ta kara bude kofa ga kasashen ketare da yadda kasar ta ke samar da muhalli mai kyau ga jarin waje duk sun zama abubuwan da ke jawo wa kasar jarin waje.

Duk da cewa takaddamar cinikayya da kasar Amurka ta tayar ya haifar da rashin tabbas kan tattalin arzikin duniya, wanda ya sa an samu raguwar musayar kudi a tsakanin kasa da kasa, amma fifikon da kasar Sin ke da shi kan yanayin gudanar da cinikayya ya jawo hankulan kamfanonin kasashen ketare, ta yadda kasar Sin ta ci gaba da kasancewa wurin da aka fi son zuba jari a duniya. (Mai fassarawa: Bilkisu, Ma'aikaciyar sashen Hausa na CRI)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China