Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan kayayyakin da kamfanoni masu zaman kansu na kasar Sin ke shige da ficen su ya karu
2019-09-09 10:21:06        cri
Hukumar kwastam ta kasar Sin ta sanar da wasu alkaluma, wadanda suka nuna cewa, a watanni 8 da suka wuce, yawan kudin kayayyakin da aka shige da ficen su a kasar Sin, ya kai kudin Sin RMB Yuan triliyan 20.13 adadin da ya karu da kashi 3.6% bisa na makamancin lokacin bara.

Cikinsu, darajar kayayyakin da kamfanoni masu zaman kansu suka yi shige da ficen su ta kai Yuan triliyan 8.49, adadin da ya karu da kashi 11.2% bisa na bara.

An ce, kamfanoni masu zaman kansu sun riga sun wuce matsayin kamfanoni masu jarin ketare, inda suka zama mafi samar da gudunmowa a fannin cinikin kasa da kasa. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China