Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi atisayen hadin gwiwa na bikin murnar cika shekaru 70 da kafuwar sabuwar kasar Sin
2019-09-09 13:55:35        cri
Bisa labarin da cibiyar watsa labarun murnar cika shekaru 70 da kafuwar sabuwar kasar Sin ta bayar, tun daga karfe 11 na daren ranar 7 zuwa karfe 8 na safiyar ranar 8 ga wannan wata, an yi atisayen hadin gwiwa na farko na bikin murnar cika shekaru 70 da kafuwar sabuwar kasar Sin a Tian'anmen, inda kimanin mutane dubu 90 suka halarta.

An ce, atisayen ya hada da bikin murnar, da bikin faretin soja, da jerin-gwanon fararen hula, da bukukuwan taya murnar da sauransu. A cikinsu, an yi faretin soja na tsawon awa daya, kuma an yi jerin-gwanon fararen hula, kamar yin taro da yin tafiya tare. Haka kuma an yi atisayen bukukuwan taya murnar da kuma yin gwajin tsarin wasan wuta a wurin. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China