Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Akwai masu aikin sa kai fiye da miliyan 120 a kasar Sin
2019-09-05 10:03:34        cri

Yau 5 ga watan Satumba, rana ce ta jin kai ta al'ummar Sinawa karo na 4. Babban taken ranar ta bana, shi ne mai da hankali kan yaki da talauci don inganta rayuwar jama'a. Alkaluman kididdiga da ma'aikatar kula da harkokin al'ummar kasar Sin ta fitar, sun nuna cewa, yanzu akwai masu aikin sa kai miliyan 126 da hukumomin jin kai dubu 5 da dari 5 da 11 a kasar wadanda suka yi rajista a hukumance.

A watanni shida na farkon wannan shekara, akwai gidauniyar neman taimakon kudi ta intanet guda 20, wadanda ma'aikatar ta amince da su, inda suka tara kudaden tallafi da yawansu ya kai sama da kudin Sin RMB biliyan 1.8. baki daya. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China