Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Hong Kong ta yi Allah wadai da masu zanga-zanga masu tsattsauran ra'ayi
2019-09-08 16:56:23        cri
Gwamnatin yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin, ta fitar da sanarwa a daren jiya, inda ta yi Allah wadai da kakkausar murya, kan taruwar wasu masu zanga-zanga dake da tsattsuran ra'ayi a Mong Kok da Prince Edward, don toshe hanya, da kai farmaki hukumar 'yan sanda, da kuma kunna wuta, lamarin dake kawo barazana sosai ga tsaron 'yan sanda da mazauna yankin. A sa'i daya kuma, ta bayyana godiya sosai ga ma'aikatan da suke tsayawa kan ayyukansu, don tabbatar da ayyuka sun gudana yadda ya kamata a filin jiragen sama da hanyar dogo.

Rahotanni sun ce, a cikin 'yan kwanakin da suka wuce, akwai mutanen da suka lalata gine-gine da na'urorin hanyar dogo, a ranar 7 ga wata kuma, akwai wadanda suka hana gudanar ayyuka a filin jiragen sama na kasa da kasa na Hong Kong.

Bugu da kari kuma, sanarwar ta nuna cewa, kafin hakan, kotu ta riga ta ba da umurnin haramta duk wani yunkurin hana ayyukan filin jiragen sama da hanyar dogo. Gwamnatin yankin ta yi kira ga mazauna cewa, bai kamata su nuna ra'ayoyinsu ta hanyar keta doka ba, kuma dole ne su yi la'akari da iko da bukatun matafiya da na sauran mutanen yankin. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China