Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin tana adawa da yadda kasashen G7 ke tsoma baki a harkokin Hong Kong
2019-08-27 20:07:14        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Geng Shuang, ya bayyana cewa, kasarsa ta bayyana rashin gamsuwa da kakkausar murya da ma adawa da sanarwar da taron kolin kungiyar kasashen kungiyar G7 ya fitar game da harkokin da suka shafi yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin.

Kalaman Geng na zuwa ne kwana guda, bayan da kungiyar ta fitar da wata gajeriyar sanarwar kan wasu batutuwa, ciki har da harkokin yankin na Hong Kong. Batun da kasar Sin ta sha nanatawa cewa, batun yankin, batu ne da ya shafi harkokin cikin gidan kasar Sin, kuma ba ta bukatar gwamnatin wata kasa ko kungiya ta tsoma baki a lamarin.

Jami'in ya kuma yi nuni da cewa, tashin hankalin da aka shafe watanni biyu ana yi a yankin, ya shafi zaman rayuwar mazauna, da harkokin tattalin arzikin yankin, da ma martabar yankin a idon duniya. Don haka, ya bukaci kasashen mambobin kungiyar G7, da su daina tsoma baki a harkokin yankin na Hong Kong.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China