Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An gudanar da zanga-zangar a HK domin nuna adawa da matakin Amurka na tsoma bakin cikin harkokin kasar Sin
2019-08-27 09:49:58        cri

Sama da mutane 100 ne suka gudanar da zanga-zanga jiya Litinin a gaban karamin ofishin jakadancin Amurka dake yankin musammam na HK na kasar Sin, domin nuna adawa da matakin Amurka na tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin.

Masu zanga-zangar, dauke da tutocin kasar Sin da Kyallaye suna kiraye kiraye, sun fara zanga-zangar ne da rana, daga Chater Garden dake yankin tsakiyar HK zuwa ofishin jakadancin Amurka.

Tsao Tat-ming, wanda ya shirya zanga-zangar, ya ce suna kokarin gina HK, yayin da bata-gari ke lalata ta, kuma akwai masu ingiza su. Yana mai nuna Amurka a matsayin wadda ke da hannu wajen ta'azzarar rikicin baya-bayan nan a yankin.

A cewarsa, zanga–zangar wadda mutane daga kungiyoyi daban-daban suka shiga, na da nufin yin tir da yadda Amurka ta tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin.

Masu zanga-zangar sun kuma bayyana goyon bayansu ga kokarin 'yan sandan HK na tabbatar da zaman lafiya yayin da ake tsaka da gudanar da zanga-zangar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China