Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Farfesa Zhang Weiwei: Boren da ake yi a Hong Kong ba zai yi nasara ba
2019-08-31 20:21:34        cri

A cikin watannin biyu da suka gabata, boren da masu zanga-zanga suka yi a yankin Hong Kong na kasar Sin yana kara tsanani sannu a hankali, kuma ba ga rayuwar mazauna yankin kadai ya yi tasiri mai tsanani ba, domin ya kawo cikas ga ci gaban tattalin arzikin yankin.

Yanzu haka wasu 'yan siyasa na kasashen yamma, suna sharhi kan batun Hong Kong, kuma suna tsoma baki a cikin harkokin kasar Sin, har wasu sun fito fili sun hada batun da tattaunarwar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin Sin da Amurka.

Kan wannan, farfesan kwalejin nazarin harkokin kasar Sin ta jami'ar Fudan dake birnin Shanghai na kasar Sin Zhang Weiwei ya bayyana cewa, "Yan siyasar kasashen yamma sun fi son tayar da boren juyin juya hali, amma hakarsu ba za ta cimma ruwa ba a yankin Hong Kong, inda ya yi nuni da cewa, sakamakon da aka samu bayan da aka yi bincike kan abubuwan da mazauna yankin Hong Kong ke sha'awa cikin dogon lokaci ya nuna cewa, yawancin mazauna yankin, musamman ma matasan yankin sun fi mai da hankali kan batutuwan dake shafar rayuwarsu na yau da kullum da samun guraben aikin yi da samun gidajen kwana da sauransu, yanzu wasu 'yan siyasar kasashen yamma wadanda ke da yunkurin ingiza boren juyin juya hali, suna tayar da hankalin matasan yankin domin su yi adawa ga gwamnati, ta hanyar yin zanga-zanga. Ya ce babu makawa matakin zai lalata tattalin arzikin Hong Kong, domin alkaluman da aka fitar sun nuna cewa, a halin da ake ciki yanzu, adadin mutanen da suke sauka a cikin otel-otel na yankin, ya ragu da kaso 50 bisa dari, kana adadin kudin shigar da direbobin tasi na yankin suke samu, shi ma ya ragu da kaso 50 cikin dari. Ana iya cewa, hasarar tattalin arzikin da yankin Hong Kong ya samu, ta fi hasarar da ya samu a shekarar 2008 tsanani, kuma duk wadannan sun nuna cewa, za a kammala boren ba da dadewa ba.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China