Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Taron bankunan tsakiya na Afrika yace ce-ce-ku-cen bashin Sin kan Afrika ba shi da tushe
2019-08-02 10:46:41        cri
Shugaban kungiyar bankunan tsakiya na kasashen Afrika kana gwamnan babban bankin kasar Rwanda, John Rwangombwa, ya ce, ce-ce-ku-cen da ake yadawa na batun kasar Sin tana dorawa kasashen Afrika bashi, batu ne marar tushe, ya bayyana hakan ne cikin makalar da ya gabatar a taron shekara shekara na kungiyar manyan bankunan kasashen Afrika.

Da yake jawabi a taron 'yan jaridu a Kigali, babban birnin kasar Rwanda, Rwangombwa, ya ce mafi yawan basukan da kasar Sin ke baiwa kasashen Afrika ba zai yiwu a daukesu a matsayin wata matsala ga kasashen ba.

Ya ce, yana da muhimmanci a nemi rance, kuma karbar bashi a ketare ba matsala ba ce, amma wajibi ne kasashen Afrika su tabbatar cewa sun zuba jari a muhimman ayyukan da za su taimaka wajen bunkasa tattalin arziki don samar musu da kudaden shiga daga kasashen waje, wanda hakan zai taimaka musu wajen biyan basukan da suka ciyo.

A shawarce, kamata ya yi a ciyo bashi daga cikin gida domin rage hadarin dake tattare da kudaden musaya na kasashen waje, to amma Afrika na fuskantar gibin kudade. Gwamnan babban bankin ya kara da cewa, ya kamata kasashen Afrika su inganta yanayin karba rancen kudade, su dinga karbar rance da kyakkyawar manufa, kana su sarrafa kudaden wajen gina kasuwannin hada hadar kudinsu. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China