Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rwanda ta kafa kamarori masu auna yanayin zafi a mashigar kasar domin sanya ido kan Ebola
2019-07-31 10:34:33        cri
Kasar Rwanda, ta sanya kamarori masu auna yanayin zafi a wasu wurare masu hadari na shiga kasar, domin karfafa sa ido kan cutar Ebola.

Shugaban sashen yada labarai na cibiyar binciken cututtuka ta kasar Malick Kayumba, ya ce kawo yanzu, an sanya kimanin kamarorin 12 a wasu wurare da suka hada da iyakar kasar da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, da filin jirgin saman kasa da kasa na Kigali, kuma za a kara sanya karin wasu kamarorin.

Kamarorin masu auna yanayin zafi za su tantance mutanen da mai yuwu na da zazzabi, kana za su iya ankarar da ma'aikatan lafiya dake wuraren, yana mai cewa wannan matakin zai gaggauta aikin tantance matafiya.

Jami'in ya ce, gwamnatin kasar na kokarin yin dukkan abun da za ta iya na karewa da ganowa da kuma tunkarar cutar Ebola. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China