Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yarjejeniyar sulhu za ta karfafa dangantakar Rwanda da Uganda
2019-08-22 10:55:22        cri

Wani babban jami'in kasar Rwanda ya ce yarjejeniyar fahimyar juna, wacce aka rattabawa hannu a ranar Laraba za ta taimaka wajen kawo karshen zaman tankiya tsakanin kasashen Rwanda da Uganda.

Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni, da takwaransa na kasar Rwanda Paul Kagame, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar a lokacin wani taron kolin shugabannin kasashe 4 da aka gudanar a birnin Luanda na kasar Angola, wanda ya samu halartar shugaban kasar ta Angola mai masaukin baki Joao Lourenco da na jamhuriyar demokaradiyyar Kongo (DRC) Felix Tshisekedi.

Kasashen biyu masu makwabtaka da juna sun dan samu rashin jituwa a baya bayan nan yayin da bangarorin biyu ke zargin juna game da wasu batutuwa da suke takaddama kansu, wadanda suka hada da batun tsaron lafiyar jama'a, leken asiri, da batutuwa kan iyakokin kasashen, inda matsalolin ke neman harzukan gwamnatin kasar Rwanda.

Matakin da aka dauka na cimma yarjejeniya tsakanin kasashen biyu dake shiyyar tsakiyar Afrika zai taimaka wajen kawo karshen tsamin dangantaka tsakaninsu. A wata sanarwa daga fadar gwamnatin kasar Uganda ta ce, shugabannin kasashen na Uganda da Rwanda sun amince za su mutunta ikon mulkin kai na junansu da sauran kasashen dake makwabtaka da su.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China