2019-08-10 17:11:23 cri |
Madam Akamanzi wadda ta halarci dandalin tattaunawa kan harkokin cinikayya na kasa da kasa, da kungiyar hadin gwiwar hukumomi masu zaman kansu ta kasar Rwanda ta karbi bakuncinsa a jiya, ta bayyanawa 'yan jarida cewa, aikin raya kasar Rwanda yana da nasaba da hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Sin, kuma akwai kyakkyawar makoma kan hadin gwiwar kasashen biyu.
Madam Akamanzi ta kara da cewa, Sin tana da karfi a fannonin zuba jari, da yin kirkire-kikire, da kera kayayyaki, da yawon shakatawa da sauransu. Don haka, kasar Rwanda tana son kasar Sin za ta zuba jari gare ta a fannonin samar da kayayyakin amfanin gona, da tufaffi, da kayayyakin gine-gine, da kayayyakin sadarwa da sauransu, kana tana son kara jawo hankalin Sinawa da su je kasar domin yawon shakatawa, da kuma kara fitar da kayayyakinta zuwa kasar Sin.
Shugaban kasar Rwanda da jami'ai da dama su ma sun halarci dandalin tattaunawar, inda wakilai fiye da 700 daga kasashe 23 suka halarta, ciki har da 'yan kasuwa na Sin kimanin 50. (Zainab)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China