Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Zimbabwe ya yabawa kamfanin Sin dake aikin gina sabuwar majalisar dokokin kasar
2019-06-14 12:17:54        cri

A ranar Alhamis shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya kai rangadin duba aikin gina sabuwar majalisar dokokin kasar wanda kamfanin kasar Sin ke gudanar da aikin kana ya nuna gamsuwa bisa yadda aikin ke gudana kawo yanzu.

"Na yi farin ciki bisa yadda na ga aikin ke gudana, kuma kawo yanzu babu wani abu marar dadi da ya faru. Ina fatan wannan babbar nasara zata ci gaba da dorewa har zuwa lokacin kammala aikin," shugaban kasar ya furta hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar duba aikin wanda kamfanin Shanghai Construction Group ke gudanarwa.

Ya ce, Zimbabwe tana matukar godiya ga kasar Sin saboda samar da kudaden gina sabon ginin majalisar dokokin kasar a Mt Hampden dake wajen birnin Harare, da kuma rukunin sabbin gidaje dake kusa da babban birnin kasar.

Jakadan kasar Sin dake Zimbabwe Guo Shaochun, ya ce aikin ginin sabuwar majalisar dokokin kasar na daya daga cikin manyan ayyukan da kasar Sin ta bada taimako wajen gudanarwa a nahiyar Afrika a cikin shekarun baya bayan nan.

Ya ce aikin ya zo a daidai lokacin da ake bukatarsa, saboda zai baiwa 'yan majalisar dokokin kasar Zimbabwe damar samun ingantaccen wajen tattauna muhimman batutuwan da suka shafi ayyukan majalisar domin baiwa kasar damar cimma nasarar ajandar bunkasuwar tattalin arziki a matsakaicin mataki nan da shekarar 2030.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China