Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Zimbabwe ya nada mace alkali mukamin shugabar hukumar yaki da rashawa
2019-05-31 11:15:32        cri
A ranar Alhamis shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya rantsar da mai shari'a Loice Matanda-Moyo, a matsayin sabuwar shugabar hukumar yaki da rashawa ta kasar Zimbabwe (ZACC).

ZACC, hukumar ce da aka kafa ta da nufin yaki da dukkan laifukan dake da nasaba da rashawa, rashin gaskiya, ko yi wa tattalin arziki zagon kasa, a dukkan ma'aikatu da hukumomin gwamnati da sauran hukumomi masu zaman kansu a kasar.

Job Whabira, shi ne tsohon shugaban hukumar ta ZACC, wanda aka sauke daga mukamin a watan Fabrairu bayan da shugaba Mnangagwa ya lura cewa ya gaza sauke nauyin da aka dora masa.

Za'a nada sauran mambobin hukumar nan bada jimawa ba da zarar an kammala tantance wadanda za'a dauka wanda majalisar dokokin kasar za ta gudanar a nan gaba.

Matanda-Moyo, wacce alkali ce a babbar kotun Zimbabwe, kuma mai dakin ministan harkokin wajen kasar Sibusiso Moyo, tace za ta yi yaki da rashawa iyakar gwargwadon karfinta.

"Sako na ga masu aikata rashawa shi ne su gagauta daina aikata laifukan rashawar," ta bayyana hakan ne ga kamfanin dillancin labaran kasar New Ziana bayan ta sha rantsuwar kama aikin. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China