Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Harin Bindiga a Amurka na take hakkokin bil adama
2019-08-24 16:48:29        cri

Kungiyar nazarin hakkokin bil Adama ta kasar Sin, ta wallafa wata mukala a yau Asabar, da nufin bayyana dadaddiyar matsalar harin bindiga a Amurka da aka gaza shawo kanta, wadda ta ce na take hakkokin bil adama.

Da take bayyana jerin munanan hare-haren bindiga kan jama'a da suka auku a baya-bayan nan a Amurka, mukalar ta ce, harbi kan jama'a, ya kara bayyana illar bazuwar bindigogi a Amurka, tare da bayyana matsalolin dake akwai a tsarukan siyasa da zamantakewar kasar da kuma munafurcinta kan batun kiyaye hakkokin dan Adam.

A cewar mukalar, Amurka ce ke da adadin mafi yawa na daidaikun mutane da suka mallaki bindiga a duniya. Kuma hare-hare masu alaka da harbin bindiga a kasar, sun yi sanadin mutuwar mutane 14,717 da raunatar wasu 28.172 a shekarar 2018. (Fa'iza Msuatpha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China