Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bukaci gwamnatin Afrika ta kudu ta kara binciko muhimman kasuwannin kasa da kasa a bangaren yawon bude ido
2019-08-29 09:46:32        cri
Majalisar dokokin Afrika ta kudu ta bukaci gwamnatin kasar ta kara zakulo manyan kasuwannin kasa da kasa musamman daga kasashen Sin, Indiya da Najeriya.

Ya kamata sashen kula da al'amurran cikin gidan kasar (DHA), ya lalibo wasu hanyoyi don kyautata ayyukansa game da muhimman kasuwannin duniya wadanda ake ganin su ne manyan bangarorin bunkasa fannin yawon shakatawa na kasar Afrika ta kudu, kwamitin dake kula da harkokin cikin gidan kasar ne ya bayyana hakan.

Kwamitin ya yi wannan kiran ne bayan da ya kammala ziyarar duba wasu muhimman ayyuka na tsawon kwanaki 4 a babban ofishin hukumar ta DHA dake birnin Pretoria da sauran rassan hukumar.

Fannin yawon bude ido yana daya daga cikin muhimman ginshikan da shugaban kasa Cyril Ramaphosa ya sha alwashin ingatawa da nufin bunkasa tattalin arzikin kasar. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China