Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
IMF: GDPn Afirka ta kudu zai karu da kaso 0.7 a shekarar bana
2019-07-24 11:21:35        cri

Asusun ba da lamuni na IMF ya yi hasashen cewa, a bana ma'aunin tattalin arziki na GDPn Afirka ta kudu, zai karu da kaso 0.7 bisa dari.

Cikin wani rahoto da asusun ya fitar a jita Talata, ya ce a shekarar 2018 da ta gabata, kasar ta samu karuwar kaso 0.8 bisa dari ne. IMF ya ce koma bayan da kasar ta samu a wannan fanni, ya biyo bayan kalubalen makamashi da kuma batutuwa masu nasaba da 'yan kwadago. To sai dai kuma IMF ya yi hasashen cewa, a shekarar 2020, ci gaban GDPn Afirka ta kudun zai kai kaso 1.1 bisa dari.

Kafin hakan, asusun ya yi hasashen karuwar GDPn kasar da kaso 1.5 bisa dari nan gaba cikin watanni 6 na shekarar bana, sai dai daga bisani ya rage alkaluman hasashen.

A daukacin shiyyar kudu da hamadar Saharar Afirka kuwa, asusun IMF ya yi hasashen cewa, a bana kasashen shiyyar za su samu karuwar kaso 3.4 bisa dari, yayin da a shekara mai zuwa kuma, ci gaban GDPn su zai kai kaso 3.6 bisa dari. Har ila yau, Najeriya za ta samu ci gaban kaso 2.3 bisa dari a bana, da kuma kaso 2.6 bisa dari a shekara mai zuwa.

IMF ya ce karuwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya, ya yiwa tattalin arzikin Angola, da Najeriya, da ma sauran kasashe dake fitar da albarkatun mai daga nahiyar Afirka kaimi. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China