Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Afrika ta kudu ya kalubalanci mai gabatar da kara ta kasar game da badakalar gudunmuwar yakin neman zabensa
2019-07-22 11:44:16        cri

Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa, ya kalubalanci mai shigar da kara ta kasar Busisiwe Mkwebane, game da zarge-zargen da ta yi masa na take dokokin aiki.

Cyril Ramaphosa ya ce rahoton na Busisiwe Mkhwebane, na kunshe da kurakurai da dama.

A ranar Juma'ar da ta gabta ne Busisiwe Mkhwebane, ta fitar da rahoton bincikenta kan badakalar gudunmuwar kudin da ya kai rand 500,000, kwatankwacin dala 36,000 da aka ba asusun yakin neman zaben shugaban kasar.

Kamfanin Bosasa wanda kuma ake kira da African Global Operations ne ya bada gudunmuwar ga ayarin yakin neman zaben Ramaphosa a shekarar 2017, karkashin Jam'iyyar ANC, lokacin Cyril Ramaphosa na matsayin mataimakin shugaban kasa.

Binciken Mkhwebane ya kuma gano cewa, da gangan Shugaba Ramaphosa ya yaudari majalisar dokokin kasar a watan Nuwamban bara, lokacin da ya shaida mata cewa, bai san cikakken bayani game da gudunmuwar da ofishin yakin neman zabensa ya karba ba.

A lokacin, shugaban ya ce gudunmuwar kudin aikin dansa ne da kamfanin ya bayar.

Amma a rahoton, Busisiwe Mkhwebane ta yi watsi da ikirarin shugaba Ramaphosa, tana mai cewa, hakkin shugaban ne bayyana kudaden da aka sanya cikin asusun yakin neman zabensa saboda ya amfana daga gudunmuwar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China