Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Minista ya bada tabbacin tsaron masu yawon shakatawa na kasashen waje a Afrika ta kudu
2019-08-09 10:22:55        cri
Ministan yawon bude ido na kasar Afria ta kudu Mmamoloko Kubayi-Ngubane, yayi kokarin bada tabbatacin tsaron lafiyar masu sha'awar yawon bude ido a kasar bayan wasu jerin cin zarafin da aka yiwa baki masu ziyarar yawon bude ido a kasar.

A yayin kaddamar da shirin gangamin wayar da kai na kasa game da tsaron masu yawon bude ido wanda ya gudana a lambun Table Mountain na birnin Cape Town, ministan ya ce, yunkurin da gwamnatin kasar ke yi na kokarin hadin gwiwa da sauran bangarori wata hujjace dake tabbatar da cewa gwamantin na yin aiki da sauran bangarori wajen tabbatar da bada kariya ga tsaron masu yawon shakatawa a kasar ta Afrika ta kudu don tabbatar da ganin kasar ta kasance a matsayin wani muhimmin wurin da zai ja hankalin masu yawon shakatawa.

Kubayi-Ngubane yace, dokokin kasa da kasa a fannin yawon shakatawa sun tabbatar da cewa yana da muhimmanci a lura da tsaron lafiyar masu yawon shakatawa a duk inda suka zaba don kai ziyara.

A watan da ya gabata, an yiwa wani mai yawon shakatawa 'dan kasar Ukrainian fashi, kana aka hallaka shi, a lokacin da yake kokarin shiga lambun shakatawa na Table Mountain dake birnin Cape Town. Birnin ya sha fuskantar matsalolin yawan fashi da makami kan baki masu yawon shakatawa a 'yan watannin da suka gabata. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China