Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jam'iyya mai mulkin Afrika ta kudu ta nuna cikakkiyar kwarin gwiwa kan shugaban kasar duk da zarge-zargen da yake fuskanta
2019-07-21 16:06:20        cri

Jam'iyyar ANC mai mulkin Afrika ta kudu ta sanar a ranar Asabar cewa tana da cikakken kwarin gwiwa kan shugaban kasar Cyril Ramaphosa wanda a halin yanzu yake fuskantar tuhuma bisa zargin rashawa game da kudaden gudunmowar yakin neman zabe.

Sanarwar ta ce, Ramaphosa yana da cikakkiyar goyon baya daga jam'iyyarsa ta ANC a kokarinsa na tabbatar da hadin kan kasar Afrika ta kudu, da kuma dakile abubuwan dake haifar da koma bayan ci gaban kasar.

Wannan mataki na zuwa ne bayan da jami'ar dake gudanar da binciken Busisiwe Mkhwebane, ta fitar da sakamakon bincikenta a ranar Juma'a, game da batun cece-kucen da ake yi na zargin mista Ramaphosa da aikata rashawa kan batun kudaden yakin neman zabe.

A cewar Mkhwebane, tawagar yakin neman zaben Ramaphosa ta amshi gudunmowar kudade da yawansu ya kai rand 500,000 kwatankwacin dala 36,000 daga kamfanin Bosasa, wanda aka fi sani da African Global Operations.

An bayar da gudunmowar ne domin tallafawa jam'iyyar ANC a yakin neman zaben shugaba Ramaphosa a shekarar 2017. A wancan lokacin Ramaphosa yana mataimakin shugaban kasa. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China