![]() |
|
2019-05-17 14:51:36 cri |
Rahoton binciken baya-bayan nan da mujallar "Nature" ta kasar Birtaniya ta fitar kan yanayin ilmin halittu da likitanci na shekarar 2019, ya bayyana cewa, sakamakon binciken da Amurka ta fitar a wanann fanni yana sahun gaba a duniya, inda kasar Sin ke biye mata baya, wadda ta samu ci gaba a wannan fanni.
Rahotanni na cewa, daga shekarar 2012 zuwa 2018, sakamakon binciken da Sin ta samu a wannan fanni ya kai matsayin biyu a duniya, inda ta dara kasashen Birtaniya da Jamus da Japan. Kuma sakamakon binciken da kasar Sin ta samu a wannan fanni ya karu da fiye da kashi 140 bisa dari bisa na shekarar 2012. (Amina Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China