Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hukumar hada-hadar hannayen jari na kamfanonin kimiyya da fasaha ta fara aiki
2019-07-22 10:46:09        cri

Hukumar hada-hadar hannayen jari ta kamfanonin kimiyya da fasaha ta kasar Sin wato STAR Market, ta fara hada-hada a kasuwar hannayen jari ta Shangahai da safiyar yau Litinin, inda a kashin farko ta fara da kamfanoni 25.

A cewar shugaban hukumar kula da hannayen jari ta kasar Sin Li Chao, kafa STAR Market da kaddamar da rejistar bada hannun jari a karon farko, zai tallafawa ci gaban tattalin arzikin Sin a fannin kirkire kirkire da kuma sauya kasuwar hannayen jari.

Hukumar da aka gabatar a watan Nuwamban 2018, sabuwa ce da aka tsara domin samar da kudi kai tsaye ga kamfanonin dake aiki a bangaren manyan fasahohi, kamar fasahar sadarwa ta zamani da kayayyakin aiki na zamani da sabbin kayayyaki da sabbin makamshi da tsimin makamashi da kuma kare muhalli.(Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China