Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta bukaci Amurka ta tabbatar da furucinta kan batun HK
2019-08-20 10:14:27        cri

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bukaci Amurka ta tabbatar da furucinta kan batun Hong Kong.

Yayin taron manema labarai na ma'aikatar, an nemi kakakin ma'aikatar Geng Shuang ya yi tsokaci kan furucin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi cewa, yadda kasar Sin ta tafiyar da batun HK zai shafi tattaunawar cinikayya dake tsakanin kasashen biyu, inda kakakin ya ce batun HK batu ne cikin gidan kasar Sin. kuma a baya, shugaba Trump ya taba cewa, HK bangare ne na kasar Sin, kuma za su magance batun da kansu, ba sa neman shawara. A don haka, Sin ke fatan Amurkar za ta tabbatar da furucin.

A cewar kakakin, abu mafi muhimmanci da ya shafe komai a yanzu shi ne, dakatar da zanga-zanga da dawo da doka da oda a yankin HK.

Ya kara da cewa, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin, na goyon bayan kantoma Carrie Lam wajen jagorantar gwamnatin yankin musamman bisa tanadin doka, haka zalika, tana goyon bayan 'yan sandan yankin wajen tabbatar da doka tare da hukunta masu tada rikici. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China