Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a kafa gwamnatin hadaka a Sudan
2019-08-21 10:10:43        cri
Kwamitin mulkin soji na Sudan, ya amince da kafa majalisar mulkin kasa na hadin gwiwa mambobi 11, a jiya Talata.

Kakakin kwamitin soji, Shams-Eddin Kabashi ne ya bada sanarwar, kwana 1 bayan gurfanar da tsohon shugaban kasar, Omar al-Bashir a gaban kotu bisa zargin cin hanci.

Sham-Eddin Kabashi ya sanar yayin wani taron manema labarai a jiya cewa, kwamitin ya fitar da dokar da ta kafa gwamnatin hadaka, karkashin shugabancin Lt. Janar Abdel Fattah Al-Burhan.

A yau Laraba ne Abdel Fattah Al-Burhan zai sha rantsuwar kama aiki a gaban alkalin alkalan kasar, yayin da su kuma mambobin gwamnatin za su yi rantsuwar a gabansa.

Kakakin ya kara da cewa, a yau din ne kuma, za a nada firaminista, inda zai yi rantsuwar kama aiki a gaban shugaban gwamnatin da kuma alkalin alkalan kasar.

Da farko, kungiyar kawancen 'yan adawa ta Freedom and Change Alliance, ta amince da nada babban masanin tattalin arziki na kasar, Abdalla Hamdok a matsayin Firaminista. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China