Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sudan ta bukaci Amurka ta tsameta daga sahun kasashen dake daukar nauyin ta'addanci
2019-08-07 10:43:34        cri
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sudan a jiya Talata ta bukaci gwamnatin kasar Amurka data tsame kasar Sudan daga cikin jerin kasashen dake daukar nauyin ayyukan ta'addanci.

Ma'aikatar harkokin wajen Sudan ta nemi wannan bukata ne karkashin jagorancin jami'in ma'aikatar Omer Dahab, wanda ya bayyana hakan a lokacin taron tattaunawa da wakilin musamman na kasar Amurka dake Sudan Donald Booth a birnin Khartoum.

A cewar Dahab, a halin yanzu kasar Sudan tana neman matakan da zata daga matsayinta a harkokin kasa da kasa, ya kara da cewa, Sudan tana bukatar goyon bayan al'ummar kasa da kasa domin cimma nasarar shirin samar da dawwamamman cigaba na MDD nan da shekarar 2030.

Ya kara da cewa, kasar Sudan tana bukatar kyautata dangantakarta da kasar Amurka da ma sauran kasashen duniya, dangantakar wadda ta yi tsami a tsakaninsu cikin gwamman shekaru.

A nasa bangaren, wakilin na Amurka ya ce Washington tana aiki da abokan huldarta domin duba yadda za'a tallafawa kasar Sudan. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China