Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta ba da takardu biyu don sa kaimi ga bude kofa da hana keta doka
2019-08-23 15:19:46        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar kasuwancin kasar Sin Gao Feng, ya shaidawa manema labarai a jiya Alhamis cewa, Sin za ta gabatar da sabon takardar jerin kamfanonin waje da aka haramtawa shiga kasuwar kasar, da kuma takardar jerin kamfanoni maras inganci. Takarda ta farko za ta magance batun shigo da jarin waje yadda ya kamata da kawar da shingen da ba a iya gani da ido a wannnan fanni. Takarda ta biyu kuwa, za ta yi yaki da kamfanonin waje da kungiyoyin waje da kuma daidaikon mutane, wadanda suka keta ka'idar kasuwa da ta yarjejeniya, da kuma daina samarwa kasar Sin kayayyaki bisa wani dalili da ba na ciniki ba, har ma da kawo babbar illa ga kamfanonin kasar Sin, kana da kawo barazana ga tsaron kasar.

Wadannan takardu biyu sun bayyana niyyar kasar Sin na kara bude kofarta ga kasashen waje. Takarda ta biyu ta kiyaye tsaron kasar, da muradu mai dacewa na kamfanoni da moriyar al'umma, haka kuma ta kiyaye ka'idar tattalin arziki da ciniki na duniya da tsarin yin ciniki tsakanin bangarori daban-daban. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China