Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kungiyar AU ta jinjinawa tallafin Sin a fannin kiwon lafiya a Afirka
2019-07-30 19:30:42        cri
Jami'an kungiyar AU sun jinjinawa tallafin da kasar Sin ke bayarwa ga kasashen nahiyar Afirka, a fannin kiwon lafiyar al'ummunta.

Hakan dai ya biyo bayan kaddamar da filin da zai kasance harabar ginin cibiyar kandagarkin yaduwar cututtuka ta nahiyar Afirka, wadda kasar Sin za ta ba da tallafin ta a yayin ginawa.

A ranar Litinin ne dai wakilai daga ofishin helkwatar kungiyar ta AU, da jami'an gwamnatin kasar Habasha, da jami'an ofishin jakadancin Sin dake Habashan, suka hallara a harabar wannan fili dake kudancin birnin Addis Ababa domin kaddamar da shi. Ana sa ran nan ba da dadewa ba, za a fara gina wannan cibiya a filin mai fadin sakwaya mita 90,000.

An kuma tabbatar da cewa, aikin daya ne daga alkawuran da kasar Sin ta gabatar ga al'ummun kasashen nahiyar Afirka a shekarar bara.

A yayin taron dandalin tattauna hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka na watan Satumbar shekarar bara da ya gudana a birnin Beijing ne dai, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya sanar da cewa, Sin ta daga matsayin wasu ayyukan tallafin kiwon lafiya 50 da take aiwatarwa a Afirka, musamman ma muhimman cikin su, kamar aikin gina cibiyar kandagarkin yaduwar cututtuka ta nahiyar Afirka ko CDC a takaice.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China