Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta fara zaman makokin kwanaki uku don karrama marigayi shugaban kasar Tunisiya
2019-07-28 16:06:03        cri
Kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta bayyana sakon ta'aziyyar mutuwar marigayi shugaban kasar Tunisiya Beji Caid Essebsi.

Kungiyar ta Afrika mai mambobin kasashe 55, ta bayyana sakon ta'aziyyar rasuwar shugaban kasar ta arewacin Afrika Essebsi cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar, sannan ta sanar da yin makokin na kwanaki uku domin karrama irin abin koyin da fitaccen dan siyasar na kasar Tunisia ya bari.

Daga cikin kwanaki ukun na zaman makokin, an sauko da tutar kungiyar AU kasa kasa a harabar helkwatar kungiyar dake Addis Ababa na kasar Habasha tun daga ranar Asabar.

Dan siyasar wanda ya jima yana gwagwarmaya ya rasu ne a ranar Alhamis yana da shekaru 92.

A ranar Juma'a, ma'aikatar harkokin cikin gidan Tunisia ta sanar da cewa ta yi wani gagarumin shirin da ba'a saba ganin irinsa ba a yayin gudanar da jana'izar marigayi Essebsi, marigayin ya fara shiga harkokin siyasar kasar ne tun a shekarun 1941. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China