Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kafa dokar ta-baci a gabashin Chadi bayan barkewar fadan kabilanci
2019-08-19 09:33:08        cri

A jiya Lahadi shugaban kasar Chadi Idriss Deby, ya kafa dokar ta-baci ta tsawon watanni uku a gabashin lardunan Sila da Ouaddai, inda aka samu barkewar fadan kabilanci a kwanan nan wanda ya yi sanadiyyar mutuwar gwamman mutane.

An bada sanarwar ne bayan ziyarar da shugaba Deby ya kai zuwa yankin Goz Beida dake lardin Sila. Ministan tsaron kasar zai tabbatar da an aiwatar da dokar ta-bacin da gwamnatin ta kafa.

Domin kawo karshen yanayin tashin hankalin da ake fuskanta, tuni shugaban kasar ya bada umarnin tura bataliyar sojoji tare da ba su umarnin kwace dukkan makaman dake hannun fararen hula a yankin.

Shugaba Deby ya ce, babban dalilin da ya haddasa matsalar shi ne yin fasa kaurin makamai zuwa sassan kasar.

Ya kara da cewa, an dorawa jami'an tsaro alhakin daukar kwararan matakai domin kwantar da tarzomar, da kuma dakile duk wani yunkurin tada rikicin masu dauke da makamai a sassan kasar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China