Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 37 sun mutu a sakamakon rikicin kabilu da ya faru a gabashin Chadi
2019-08-10 17:14:22        cri
Shugaban kasar Chadi Idriss Deby ya bayyana a jiya cewa, mutane 37 sun mutu a sakamakon rikicin kabilanci da ya barke a jihar Ouaddai dake gabashin kasar.

Shugaba Deby ya dora alhakin barkewar rikicin kabilancin kan shigar da makaman kasar, daga kasar Libya da sauran kasashe ba bisa ka'ida ba. Kuma shigar makaman kasar ne, wasu tsageru sun kai hari ga jami'an tsaron gwamnatin kasar a jihar Ouaddai da jihar Sila.

Shugaba Deby ya bayyana cewa, gwamnatin kasar ta riga ta dauki matakan warware matsalar dake tsakanin kabilun kasar tare da yaki da jigilar makamai ba bisa ka'ida ba.

Ko a watan Mayun bana, mutane 22 sun mutu a sakamakon rikicin kabilanci da ya faru a jihar Sila, yayin da wasu tsageru ne suka kai hari ga wani kauyen dake jihar Ouaddai, wanda ya haddasa mutuwar mutane 12. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China