Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Harin kunar bakin wake ya yi sanadin rayuka akalla 6 a yammacin Chadi
2019-08-15 09:13:53        cri

Mutane akalla 6 ne suka rasa rayukansu a wani harin kunar bakin wake da safiyar jiya Laraba a yankin Kaiga Kindjiria dake lardin Lac, na yankin yammacin Chadi.

Lardin na kan iyaka da Nijeriya, wadda ke zaman maboyar kungiyar Boko Haram, da kuma Chadi da Kamaru. An shafe kimanin shekaru 10 ana fama da ayyukan masu ikirarin Jihadi a wadannan yankunan iyaka.

Ko a tsakiyar watan Afrilun da ya gabata, sojojin Chadi sun harbe 'yan ta'adda 63 a yankin na Kaiga Kindjiria, a wani samame da suka kai kan kungiyar Boko Haram a kasar. An kuma kashe sojoji 7 yayin arangamar.

Tun daga lokacin zafi na shekarar 2015, aka kafa dakarun kawance na kasashen Benin da Chadi da Kamaru da Nijar da Nijeriya, da nufin karfafa hadin gwiwar yaki da Boko Haram a yankin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China