Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Habasha ta kaddamar da sabon shirin inganta shigar da mata bangaren kimiyya da fasaha
2019-06-05 11:30:51        cri
Ma'aikatar kula da harkokin kimiyya da fasaha ta Habasha, ta kaddamar da wani sabon shiri a jiya Talata, dake da nufin inganta shigar mata sana'o'in dake da alaka da kimiyya da fasaha.

Sanarwar da ma'aikatar ta fitar, ta ce sabon shirin na da nufin inganta mata masu sana'o'i a bangaren fasaha da kimiyya, ta hanyar bada horo ga matan da suka fito daga sassa daban-daban na kasar dake gabashin Afrika.

Ta ce sabon shirin, wanda sakamako ne na hadin gwiwa tsakanin ma'aikatar kula da harkokin kirkire-kirkire da fasaha da cibiyar bincike ta Entoto dake da mazauni a kasar, zai bada horo a kashin farko, ga mata 25 da suka hadu a Addis Ababa, babban birnin kasar.

Daraktar sashen kula da harkokin mata da matasa ta ma'aikatar, Elisabeth Gebreselassie, ta bayyana yayin kaddamar da shirin cewa, Gwamnatin kasar ta kuduri niyyar inganta damawa da mata a bangaren, la'akari da ci gaban fasaha da ake samu kullum a fadin duniya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China