Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan kayayyakin da masanaantun kasar Sin suka samar ya karu da kaso 4.8 a watan Yuli
2019-08-14 14:15:13        cri

Hukumar kididdiga ta kasar Sin ta bayyana a yau cewa, yawan kayayyakin da masana'antun kasar suka samar, wanda ke da muhimmanci ga ma'aunin tattalin arziki, ya karu da kaso 4.8 a watan Yuli.

A cewar hukumar, karuwar ta yi kasa da wanda aka samu a watan Yuni da kaso 1.5.

A cikin watanni 7 na farko na bana, yawan kayayyakin da masana'antu suka samar ya karu zuwa da kaso 5.8 a kan na shekara 1 da ta gabata, inda ci gaban ya sauka daga kaso 6 da aka samu a rabin farkon bana.

Ana amfani da mizanin yawan kayayyakin da ake kira darajar masana'antu a hukumance ne wajen auna wasu kamfanoni dake cinikin a kalla yuan miliyan 20, kwatankwacin dala miliyan 2.8 a ko wace shekara.

Yawan kayayyakin da aka kera kuwa, ya karu zuwa kaso 4.5 a kan na bara, wanda ya ragu da kaso 6.2 a watan Yuni, yayin da na bangaren hakar ma'adinai ya sauka zuwa kaso 6.6 daga kaso 7.3 a watan Yuni.

Bangaren kera kayayyakin fasaha na zamani kuwa ya ci gaba da samun tagomashi, inda kayayyakin da ya samar ya karu zuwa kaso 6.6 a watan da ya shude. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China