Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ce ke kan gaba cikin jerin abokan cinikayyar Algeria a rabin farkon bana
2019-08-14 09:49:23        cri

Hukumar kwastam ta kasar Algeria, ta ce kasar Sin ce a kan gaba cikin manyan abokan cinikayyarta a cikin rabin farko na bana.

Sanarwar da hukumar ta fitar a jiya, ta ce kasar Sin ce a gaba wajen shigar kayayyakinta kasar Algeria, wadanda darajarsu ta kai dala biliyan 4.22, ko kuma kaso 19 na jimilar kayayyakin dake shiga Algeria daga ketare.

Kasar Faransa ce ta biyu a wajen shigar da kayayyaki Algeria, wadanda darajarsu ta kai dala biliyan 2.14, sai Spaniya dake rufa mata baya, Jamus ce ta 4, sai kuma Italiya a mastayi na 5.

A bangaren da Algeria ke kai musu kayayyaki kuwa, Faransa ce ta daya da kayayyakin da darajarsu ta kai dala biliyan 2.66, Italiya ce ke bi mata, sai Spaniya, sannan Amurka. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China