Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin da Algeria sun kafa ingantaccen hadin gwiwa karkashin shawarar "ziri daya da hanya daya"
2019-06-21 10:08:36        cri

Kasashen Sin da Algeria sun kafa kyakkyawan hadin gwiwa karkashin shawarar "ziri daya da hanya daya" (BRI), jakadan kasar Sin a Algeria Li Lianhe, shi ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa kwanan nan da Jaridar Le Jeune Ind├ępendant dake Algeria.

Li ya bayyana cewa, "kasashen sun yi nasarar kafa hadin gwiwar siyasa, tattalin arziki, cinikayya, raya al'adu da sauransu, inda aka samu kyautatuwar fahimtar juna da amincewar juna ta fuskar siyasa da mutunta juna."

Algeria ta kasance kasa ta biyar mafi girma a Afrika ta fuskar huldar cinikayya da kasar Sin, karfin jarin kasuwancin dake tsakanin kasashen biyu ya kai dala biliyan 9.1 a shekarar 2018, in ji jakadan na kasar Sin.

Li ya ce, dangantakar Sin da Algeria a cikin shekaru 60 da suka gabata ta kasance abin misali na dangantakar hadin gwiwa dake tsakanin Sin da kasashen Larabawa.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China