Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 5 sun mutu yayin murnar tsallakewar da Algeria ta yi zuwa matakin karshe a gasar AFCON
2019-07-16 10:01:17        cri

A kalla mutane 5 ne aka tabbatar da mutuwarsu kana wasu 13 suka samu raunuka a wani hadarin da ya afku a gabashin Algeria a daidai lokacin da ake murnar nasarar da kasar ta arewacin Afrika ta samu na kaiwa matakin karshe a gasar cin kofin kasashen Afrika ta (AFCON) a kasar Masar.

Gidan radiyon kasar ya sanar da cewa, lamarin ya faru ne a cikin daren ranar Lahadi a gabashin lardin Jijel a lokacin da wata babbar mota ta yi karo da motar dake dauke da wasu magoya bayan kungiyar wasan kwallon kafan Algeria, bayan da kasar ta yi nasara a kan Najeriya a wasan kusa da na karshe a gasar AFCON.

Magoya bayan kungiyar wasan su biyu sun mutu nan take, yayin da mutane 3 suka mutu a asibiti.

Majiyar ta kara da cewa, wasu mutane 13 da suka ji rauni suna cikin matsanancin hali inda ake kula da su a asibiti. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China