Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Algeria na rikon kwarya zai shirya tattaunawa ba tare da wakilan gwamnati ko sojoji ba
2019-07-04 10:48:03        cri

Mai rikon kwaryar shugabancin kasar Algeria Abdelkader Bensalah, a jiya Laraba ya sanar da tsara wata cikakkiyar tattaunawa mai zaman kanta ba tare da shigar da jami'an gwamnati da na sojojin kasar ba.

Bensalah ya bayyana cikin wani jawabin da ya gabatarwa 'yan kasar ta gidan talabijin na kasar cewa, ya bukaci dukkannin masu ruwa da tsaki a harkokin siyasar kasar da su shiga tattaunawar wadda gwamnatin kasar za ta kaddamar domin tattaunawa game da zaben shugaban kasar dake tafe.

Ya kara da cewa, an shirya taron tattaunawar ne ga dukkan jam'iyyun siyasar kasar, da kungiyoyin fararen hula, da kungiyoyin kwadago, da wakilan kungiyoyin masu zanga zanga wadanda suka fara tun a watan Fabrairu.

Mutane masu daraja da kima 'yan ba ruwanmu wadanda ba su da ra'ayin wata jam'iyyar siyasa ko sha'awar tsayawa takarar siyasa su ne za su jagoranci tattaunawar, in ji Bensalah.

Bensalah ya kara da cewa, manufar shirya tattaunawar ita ce, domin shirya sahihi kuma ingantaccen zabe a kasar, ya kara da cewa, kafa wata hukuma mai zaman kanta wadda za ta sanya ido game da yadda zaben kasar zai gudana yana daga cikin manyan ajandodin shirya taron tattaunawar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China