2019-05-14 09:49:42 cri |
Wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar, ta ce akwai yuwar 1 cikin mutanen 2 da suka mika wuya ya shiga kungiyar ta'addanci ne a shekarar 2011, yayin da dayan kuma ya shiga a shekarar 2015, inda kuma ta ce suna dauke da bindigogin ruwa samfurin Kalashnikov guda 2.
Aljeria ta bude hanya a kan iyakarta ta kudanci, domin karfafawa tsagerun kasar da suka shiga kungiyoyin ta'adda gwiwar ajiye makamansu, domin a yi musu shari'a mai adalci.
Yanayin kasar Aljeria ya kyautata sosai cikin shekaru 10 da suka gabata, sai dai har yanzu a kan samu arangama tsakanin jami'an tsaro da kungiyoyin 'yan ta'adda. (Fa'iza Mustapha)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China