Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD: Boko Haram ta hallaka mutane 27,000 a Najeriya a hare haren ta'addancin shekaru 10
2019-08-02 10:41:49        cri
A bisa wasu alkaluman da MDD ta fitar, an ce, sama da mutane 27,000 kungiyar Boko Haram ta kashe a Najeriya tun bayan da ta fara kaddamar da hare haren ta'addanci a shiyyar arewa maso gabashin kasar a shekarar 2009.

Wata sanarwa da aka baiwa kofenta ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Abuja, ta rawaito jami'in shirin ba da agajin jin kai na MDD dake Najeriya, Edward Kallon, yana cewa, kimanin wasu sabbin adadin mutane 130,000 ne rikicin ya tilastawa ficewa daga gidajensu.

Ya ce rashin tsaro a 'yan watannin baya bayan nan yayi sanadiyyar tilastawa mutane sama da 130,000 sake yin kaura zuwa sansanonin 'yan gudun hijira inda suke neman taimako da kuma kariya. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China